Explore every episode of the podcast Mahangar Mu
| Title | Pub. Date | Duration | |
|---|---|---|---|
| 35 - Tsadar Rayuwa: Sabubba Da Mafita | 22 févr. 2024 | 00:23:04 | |
Kasancewar yanzu kayan masrufi sun yi tsada. An samu hauhawan farashi a dukkan abubuwan da zasu samar da ingantacciyar rayuwa. Menene sabubba sannan ina mafita.
| |||
| 34 - Haraji Don Yin Sallah | 11 déc. 2023 | 00:13:04 | |
A doron ƙasa, mallaka Allah an samu wata nahiyar da idan kayi Sallah a fili bainar jama'a, sai ka biya harajin Euro Ɗari Biyu (sama da Naira Dubu Ɗari da Saba'i a yau da 11/12/2023).
Ga kuma tubka da warwara a aiwatar tsare-tsare da suka yi na Ƴancin ɗan Adam da suke ikirarin yi.
Mu samu damar tattaunawa da Mohammed Moayad al-Rachid da ya zauna a wannan ƙasar don jin yadda ya rayu a matsayin sa na Musulmi.
| |||
| 33 - Bankin Abinci | 25 nov. 2023 | 00:13:04 | |
Yadda muke da Banki don ayijar kudi, akwai hanya da wasu masu himma suke amfani da ita wajen tanada abinci don taimaka wa mabukata a lokaci da a ke matukar buqata.
Mun tattauna da wani kwararre a fannin noma da kiwo wanda ya kwashe shekaru masu yawa yana aikin gona da ta kai hectare 350. Kuma masani ne kwarai wajen harkar bada tallafi da gudanar qungiyoyin agaza wa gajiyayyu da mabuƙata.
Mun samu zama da Mal. Muzzammil Abdullahi (Abu Nadia) don ƙarin haske akan taimaka wa mabuƙata a halin da muka tsinci kan a wannan duniyar. BANKIN ABINCI
| |||
| 32 - Wuce Gona da Iri | 06 mai 2023 | 00:15:44 | |
An samu wani da ya ke ganin ya fi Annabi ilimi da iya adalci, don haka ba abin mamaki ba ne ko yaushe kuma a ko ina, a samu wasu da suke ganin ilimin su ya kai matsayin da hatta Malaman su, ba su ganin su da gashi a ido. | |||
| 31 - Malamai Da Zamanin Su | 30 avr. 2023 | 00:16:07 | |
Malamai da suka wallafa littafai a baya, sun duba yanayin al'umarsu ne da buqatuwar al'umar tasu ga wannan littafai da suka rubuta, shi ya sa suka wallafa su. Misali idan ka duba irin su Aqida Wasitiyyah, Aqida Hamawiyyah da su Tadmuriyyah, ai duk daga sunayen garuruwa ne aka basu suna, Ibn Taymiyyah ya wallafa su ne musamman ga mutanen wadannan wurare. | |||
| 30 - Abin Kwaikwayo | 20 avr. 2023 | 00:14:30 | |
Shin laifi ne in kwaikwayi wani? Akwai wasu sinfin mutane da Shari'a ta yadda in kwaikwaya ne? Mun tattauwa akan wannan mas'ala ganin cewa musamman matasan, suna duba zuwa ga wasu mutana ne suna kwaikwayon irin rayuwar su. | |||
| 29 - Kutse Cikin Ilimi | 06 avr. 2023 | 00:16:14 | |
Wannan karo, mu taɓo fanni ne da ta shafar ilimi na Addini da irin kutse da katsalandar da za ka ga wasu na yi a cikin ilimi. Ɗanuwa Mal. Abbas Tijjani ya yi magana kan yadda magabata suke bada ƙima da nuna ladabi ga ilimi. Ku sauraa
| |||
| 28 - Ciyarwa Da Ginin Al'umma | 30 mars 2023 | 00:12:58 | |
Yadda muke ƙoƙari wajen ciyar da mabuƙata a watan azumi, da haka muke huɓɓasa wajen ganin mun ciyar a watannin da ba Ramadan ba, da abin ya yi kyau. Abin da zai fi wannan shi ne a gina al'umma wadda adadin wanda ake ciyarwa kullum raguwa suke yi.
| |||
| 27 - Ga Ki Uwa Kuma Ga Azumi | 23 mars 2023 | 00:16:17 | |
Wannan ne karo na farko da muka tattauna da macce. Ganin cewa wantan Azumi ya kama, mata da yawa suna dukufa wajen aikin neman Aljanna ta hanyar hidima da gida, miji, yara da kuma babban abin, wato Ibada. Shin wai wadannan matan, ya ya suke yi ne ganin cewa kema Allah Ya azurta ta da aure, yarinya kuma tana kasuwancin ta? Ku saurari tattaunawar mu da Fatima Zarah Maitambari | |||
| 26 - Shirin Ramadan | 16 mars 2023 | 00:12:06 | |
Yadda watan Ramadan ya gabato, yana da kyau a ce mutum ya gama duk wata shiri da ya ke tunanin ya yi yanzu. A wannan tattaunawar, mu yi magana kan wani muhimmin abu da ya kamata a ce mu sani game da Rayuwar mu da kuma Ramadan | |||
| 25 - Ra'ayi Ko Addini? | 09 mars 2023 | 00:12:17 | |
Yau mutane da yawa suna fifita ra'ayin su abisa abin da Addini ya karantar, yin haka kuma matsalolin da ya ke haifarwa na da yawa.
| |||
| 24 - Rigakafi Yafi Magani | 03 mars 2023 | 00:13:33 | |
Musulmi mun zama mutane da sai abu ya faru sannan muke neman daukar mataki. Haka kuma na nuna rashin wayewa ne da kuma ci baya. Kamata ya yi a ce kafin abu ya faru, mun riga mun tanada abubuwa da za su tinkari abin. In alheri, alheri in kuma sharri, rigakafi. Allah bamu iko gyarawa, amin. Ayi sauraro lafiya. | |||
| 23 - Wa Za Ka Zaba? | 23 févr. 2023 | 00:14:07 | |
Mun tattauna yadda al'amura suke yanzu musamman kasancewar lokaci ne na zabe. Shin wai me ya kamata mu yi a matsayin mu na Musulmi? Ina muka dosa sannan gaba wace irin shiri zamu yi ne? Saurara ku ji hirar ta mu. | |||
| 02 - Representing Islam | 06 nov. 2020 | 00:20:03 | |
This discussion was centered on Muslims and the way they go about their daily lives and the impact this has on how people regard their religion of Islam. The reality is that a lot people form their perception and judgement of Islam on the way they see Muslims behave. So the big question is HOW ARE YOU REPRESENTING ISLAM? Two powerful stories were told in the episode relating to how Islam is represented and alternatives are given where relevant. The highlight of this podcast is for all Muslims to be aware that they are representatives of the Deen in the public realm. Enjoy listening!
| |||
| 01 - Being Kind To Others | 03 oct. 2020 | 00:21:44 | |
In this podcast, we explored the major reason why people are lacking when it comes to the issue kindness, also we spoke about some of the benefits that comes with being kind as Islam teaches.
| |||
| 22 - Haqqin Dan Adam A Musulunci | 24 févr. 2020 | 00:24:37 | |
Shin wa menene mahangar Addini akan yancin haqqin Dan Adam da ake ta magana? Saurari wannan tattaunawa don samun haske akan wannan maudu'i
| |||
| 21 - Rayuwa Mai Sauqi | 01 févr. 2020 | 00:21:28 | |
Idan kana so ka samu rayuwa mai dadi, Maza maza ka saurari wannan don cikin mintoci kadan, mun tattauna yanyar samun irin wannan rayuwar.
| |||
| 20 - Tsarin Jari Hujja | 25 janv. 2020 | 00:18:12 | |
Sai mu ji ana ce wai jari hujja, to shin hakan kuskure ne ko dai bamu fahinci abin a ne.
| |||
| 19 - Nau'ukan Ilimi | 17 janv. 2020 | 00:19:47 | |
Shin wasu fannonin ilmuka aka bar musulmai a baya da ya kamata su farka. Akwai bambanci tsakanin ilimin fiqihu da ilimin da na kiwon lafiya da sauran su?
| |||
| 18 - Malamai da Siyasa | 11 janv. 2020 | 00:24:55 | |
Shin akwai rawar da malamai ya kamata su taka a yanayin yadda ake siyasa a yau, ba wannan ba ma, shin ya kamata malamai su shiga siyasa kuwa? Wai menene Zuhudu sannan malamai kaɗai aka sani da zuhudu? Aibi ne idan aka samu malami ya yi Kuɗi? Don samun ansar waɗannan tambayoyi, saurari wannan shiri...
| |||
| 17 - Shaye Shaye Cikin Al'umma | 02 déc. 2019 | 00:17:09 | |
Dr. Mansur Sokoto ya bamu lokaci don tattaunawa kan matsalar shaye-shaye. Wallah Shaye-Shaye babbar matsala ce da mutanne ke daukan ta qarama. Lokacin da mukayi nazarin illoli da ci baya da wannan mugunyar dabi'a ke tattare da ita, to fa nan take zamu fahihimci cewa ta wuce duk tunanin mu. A wannan tattaunawar, Dr. ya bayyana mana menene kayan maye, yadda ake gane dan shaye-shaye da hanyoyin rigakafi da magance wannan matsalar shaye-shaye. Ku ba mu mintoci kadan don sanin "Mahangar Mu" | |||
| 16 - Degree, Sana'a Da Aiki | 25 nov. 2019 | 00:19:52 | |
Yau matasa da dama sun kamma karatu amma ba abin yi. Shin wai manene matsalar ne? Wai ina aka kuskure sannan ina mafita? Saurari wannan maqala don jin Mahangar Mu. | |||
| 15 - Karance-Karance | 18 nov. 2019 | 00:21:27 | |
Rayuwar Musulmi fa yanzu dole akwai buƙatuwar ya faɗaɗa karatun sa don ire-iren ra'ayoyi da ake ta ƙoƙarin yaɗawa suna da yawa kuma idan mutum bai san su ba, bai asalin su ba, bai san irin illoli ko alfanu da musulmi zai samu ba, to lallai za a bar shi a baya. Wannan tattaunawa, anyi ta ne don fahimtar da al'uma Mahanga da ya kamata a fahimci waɗannan ra'ayoyin.
| |||
| 14 - Ina Laifi Na? | 11 nov. 2019 | 00:16:20 | |
Sau da yawa, sai ka ga ana wa mutum wani irin kallo, hatta ta waje mu'amalantar sa, sai a munana masa.
In ka duba, za ka ga wata qila shima yana da laifi da a tunanin sa ba wani laifi ba ne, kuma amma har a gaban Allaah,
yana iya samun alhaki don shi ya janyo hakan.
Wannan kuma yafi samuwa ga mata, kuma zaka ga daga iyaye ne wasu lokutan.
Ku saurari wannan tattaunawa da muka yi don jin "Mahangar Mu" akan matsalar.
| |||
| 13 - Murna Ko Hisabi? | 07 nov. 2019 | 00:18:56 | |
Ga wata matsala da aka sanya shububa akan ta. Idan kana son ganin cikakken tsari da ta shafi duk wani fanni na rayuwa, babu shakka ka dubi tsari da Annabi ya dora Sahabbai akai. Duk wata kafa wadda idan an bi ta, za a samu natija, to fa sai da ya karantar da su. Wurin da yake aibi ne kuma, ya nuna ma su, sannan ya shiryar da su tafarki wanda zasu iya gano abin da ya ke dai-dai, da kuma akasin haka. Ta wannan hanyoyin suka bi suka gano har da abin da bai fito qarara ya nuna ma su hukuncin sa ba. To kan wannan matsala, shin "Murna Zanyi Ko Hisabin Kai? | |||
| 12 - Bani Shawara | 04 nov. 2019 | 00:22:25 | |
Wannan podcast, mun tattauna kan matsaloli biyu, A yi qoqari a saurara har karshe. Sau da yawa mutane na fadawa cikin halaka saboda wani shawara da suke samu daga wasu. Aure da yawa sun mutu, jari da yawa sun karye, zumunta da yawa sun yanke duk saboda shawara da a ka basu. Mu kame bakin mu idan mun san cewa ba mu da shawarar da za mu bayar. ba dole sai mun yi magana ba idan bamu da masaniyar al'amura. | |||
| 11 - Hakan - Akwai Dalili | 28 oct. 2019 | 00:18:07 | |
Wasu lokutta, mukan ga abubuwan farin ciki sun same me, wasu lokutan kuma, abubuwa da ba mu so ke faruwa da mu. A mahangar Addini, duk abu da muka gani, to fa tabbas akwai dalilai, sai dai tunanin mu ba lallai ba ne mu hankalta da hakan. Rashin haihuwa, mutuwa, samun dukiya, ganin saɓanin Addu'o'i da muka yi ne da dai sauran su. Saurari 'MAHANGAR MU'
| |||
| 10 - Zaman Aure | 15 oct. 2019 | 00:20:38 | |
Wai aka ce "Zo mu zauna, zo mu saba". Shin wannan matsalar wani shawara ne a Mahangar ka, kake gani zata yi aiki don sasanta sabanin maaurata tunda dai rayuwa ta tabbatar mana inganci wannan magar da muka kawo. Mu dai, idan ka saurari wannan shiri, za ka fahimci Mahangar Mu. | |||
| 09 - Neman Aure 3 | 15 oct. 2019 | 00:20:32 | |
Kun taba la'akari da yadda muke gudanar da bukukuwan mu yau kuwa? Menene laifi ko kurakurai da muke yi a hidimar bikin mu? Wasu abubuwa ne laifi ba da muke yi? Shin menene haduran laifukan da muke yi a rayuwar aure bayan buki? Yaya zanyi in gyara matsalar da na riga na jefa kaina a ciki? Ku saurari Mahangar Mu don samun amsoshin wadannan tambayoyi. | |||
| 08 - Neman Aure 2 | 15 oct. 2019 | 00:12:41 | |
To bayan mutum ya/ta samu wanda za a aure, me ya kamata ayi ne? | |||
| 07 - Neman Aure 1 | 15 oct. 2019 | 00:13:22 | |
Wai shin yaya ya kamata a nemi aure ne? Shin muna yi daidai kuwa? Ina laifin abin da na ke yi? | |||
| 06 - Malamai da Ilimi | 15 oct. 2019 | 00:13:26 | |
Anya yau kuwa ana ba ilimi muhimmmanci kamar yadda magabatanmu suka ba da kuwa? Amma wani lokaci, sai kaga kamar ba laifin mu ba ne. Saurari wannan shirin don sanin Mahangar Mu. Bamu aron kunnuwar ka. | |||
| 05 - To Fa Iyaye | 15 oct. 2019 | 00:12:57 | |
Wannan shin qalubale ga iyaye ne ko dai kuskuren mu ne? Ku saurara don jin Mahangar Mu a wannan matsala. Ku bamu aron kunnuwar ku. | |||
| 04 - TV da Yaran Mu | 15 oct. 2019 | 00:19:04 | |
Shin wai matsala a TV a gida ne ko barin shi wa yara ko dai akwai hanyar da za abi don anfanuwa da TV? Wasu irin quguyoyi ne ke jan kwakwalwar mutane ha ya kasance sun maqale wa TV? Ku bamu aron kunnuwan ku don samun amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyin. | |||
| 03 - Tarbiyar Yara | 15 oct. 2019 | 00:12:20 | |
Idan muka duba, zamu ga cewa akwai yaduwar rashin tarbiya a cikin al'uma. Shin me ke jawo irin wannan masifa? Ina tunanin akwai abubuwa da yawa wanda ka ke tunani. Saurari wannan don samun mahangar mu a wannan matsalar. Ku bamu aron kunnuwan ku. | |||
| 02 - Lokaci Ma Yara 2 | 15 oct. 2019 | 00:11:49 | |
Idan kun saurari bayanai da muka koro a shirin baya, lallai baza ku so wannan ya wuce ku ba domin ci gaba ne.
Ku bamu aron kunnuwar ku don samun mahangar mu.
| |||
| 01 - Lokaci Ma Yara 1 | 15 oct. 2019 | 00:11:49 | |
Subhanallah, yaran mu yau suna buqatar lokacin mu amma maganar gaskiya, mun gaza wajan basu wannan babban kulawa. Wannan dabi'a kuma kan jawo matsaloli da dama. Saurara don samun cikakken bayani. | |||